Luka Modric ba na sayarwa bane-Redknapp

 Luka Modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric

Kocin Tottenham Harry Redknapp yace ba zasu sayarda Luka Modric ba, a dai dai lokacin da rahotanni ke nuna cewar dan kwallon ya mika takardar aniyarsa ta barin kulob din.

Redknapp yace bai sani ba ko dan wasan Croatia din ya mika takardar a hukumance, amma dai a cewarsa hakan baida wani amfani.

Yace"Mun san yanason tafiya, amma dai babban dan wasa ne da bama son ya barmu".

Tottenham tayi watsi da tayin fan miliyon 27 da Chelsea ta gabatar.

Modric ya shafe watanni 14 ne kacal daga cikin kwangilarsa ta shekaru shida a Spurs.

Spurs na rangadi a Afrika ta Kudu inda zasu kara da Kaizer Chiefs da kuma Orlando Pirates.