Manchester United bata zawarcin Sneijder

sniejder
Image caption Wesley Sneijder da Samuel Etoo

BBC ta fahimci cewar Manchester United bata zawarcin dan kwallon Inter Milan Wesley Sneijder don ta saye shi.

Inter dai ta karyata karbar tayi akan dan wasan, amma rahotanni sun nuna cewar United na son Sneijder ya koma kulob din.

Sai dai wasu majiyoyi daga Old Trafford sun nuna cewar babu batun sayen dan kwallon Holland din mai shekaru 27.

Phil Jones, Ashley Young da David de Gea ya koma United a cikin hutun nan.

Duk su uku sun tashi akan kusan fan miliyon hamsin da uku.

Tun bayan ritayar Paul Scholes da Ryan Giggs ake tunanin cewar United na bukatar wani dan wasa mai karfi wanda zai maye gurbinsu.