Patrick Vieira ya yi ritaya daga tamaula

 Patrick Vieira
Image caption Patrick Vieira haifaffen kasar Senegal

Tsohon dan wasan Arsenal da Manchester City da kuma Faransa Patrick Vieira ya sanarda yin ritaya daga taka leda.

Dan kwallon mai shekaru talatin da biyar an nadashi a matsayin jami'in bunkasa kwallon kafa a City.

Vieira ya bayyana cewar"Naji dadin wannan damar da aka bani kuma ina godiya ga Manchester City".

Ya kara da cewar "bani da tantama akan cewar zan bada gudumuwa wajen nasarar da kulob din zai samu".

Vieira ya kasance dan kwallo na farko da Roberto Mancini ya siya bayan zuwansa Eastlands a watan Junairu 2010.

Tarihin kwallon Vieira:

* 1994-96: Cannes - Wassanni 53 , kwallaye 3 * 1996: AC Milan - Wassani 5 * 1996-2005: Arsenal - Wassani 371 , kwallaye 32 * 2005-06: Juventus - Wassani 41, kwallaye 5 * 2006-2010: Inter Milan - Wassani 88 ,kwallaye 7 * 2010-2011: Manchester City -Wassani 39 , kwallaye 6 * 1997-2009: France - Wassani 107 , kwallaye 6