McEachran ya kulla sabuwar yarjejeniya da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Josh McEachran, yana da shekarun haihuwa 18

Matsashin dan kwallon Chelsea Josh McEachran mai shekarun haihuwa 18, ya sanya sabonta yarjejeniya da kungiyar na tsawon shekaru biyar.

Ana kallon McEachran a matsayin daya daga cikin matasan da suka taso daga kungiyar renon 'yan wasan kungiyar dake tashe a 'yan kwanakin nan.

Shima takwaransa Ryan Bertrand, mai shekarun haihuwa 22, ya sabonta yarjejeniya da Chelsea na tsawon shekaru hudu.

"Abun da nayi mafarki ne akai tun ina dan yaro, kuma ina fatan zan dade a kungiyar." In ji McEachran.

"Ina fatan zan samu taka leda a kakar wasan bana sosai."