Chelsea za ta sayi sabon gola Thibaut Courtois.

Thibaut Courtois. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thibaut Courtois.

Chelsea ta amince ta kulla yarjejeniya da golan kungiyar Genk ta Belgium Thibaut Courtois.

Courtois mai shekaru 19 zai kasance dan kwallo na farko da Andre Villas-Boas zai saya tun zuwansa Stamford Bridge.

Golan Belgium din mai shekaru 19 ya bugawa Genk wasanni 40 har ta lashe gasar kwallon kasar.

Darekta a Genk Dirk Degraen" An nuna sha'awa matuka akansa, don haka zamu barshi ya tafi".

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya tabbatar da cewar "akwai yarjejeniya tsakanin kulob din biyu, saura wasu kananan batutuwa a kamalla sasantawa".

An ganin matashin golan wato Courtois a matsayin wanda zai maye gurbin Petr Cech nan da wasu shekaru masu zuwa.