Manchester City zata bada mamaki-Clichy

clichy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gael Clichy

Sabon dan kwallon Manchester City Gael Clichy ya ce dasu za ayi kokawar neman lashe gasar Premier ta Ingila.

Dan wasan da aka siyo daga Arsenal akan fan miliyon bakwai bayan shafe shekaru takwas da gunners din, kuma ya kasance dan wasa na farko da Roberto Mancini ya siya.

Clichy yace" A kakar wasan data wuce mun kasance na uku kuma mun lashe kofin FA, a don haka akwai alamun nasarori a gaba".

Ya kara da cewar " Lokacin tafiya yayi, kuma City ne yafi dacewa".

Akan batun tsohon kulob dinsa kuwa ya nuna goyon baya ga Arsene Wenger duk da cewa Cesc Fabregas da Samir Nasri na kokarin barin kulob din.

Clichy mai shekaru ashirin da biyar ya nuna takaicinsa akan yadda Arsenal tayi mugun rawa a kakar wasan data wuce.