Corinthians ta sake tayi mai tsoka akan Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlos Tevez

Kungiyar Corinthians ta Brazil ta sake bada tayi mai tsoka akan kyaftin din Manchester City Carlos Tevez.

A farkon wannan makon ne City taki amince da tayin fan miliyon talatin da biyar akan Tevez amma a yanzu rahotanni sun nuna cewar tayin ya kai na fan miliyon talatin da tara.

Wakilin Tevez Kia Joorabchian ya shaidawa BBC cewar"Ban sani ba ko aka kara kudi a sabon tayin".

City na bukatar fan miliyon hamsin akan Tevez.

City ba zata yi gaggawar kulla yarjejeniya ba, amma idan har cinikin ya yiwu, kocin kulob din Roberto Mancini zai maida hankali wajen siyo Sergio Aguero daga Athletico Madrid don ya maye gurbin Tevez.