Arsenal zata bada Denilson aro zuwa Brazil

denilson
Image caption Denilson

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewar Denilson zai koma taka leda a Brazil.

Dan kwallon mai shekaru 23 ya koma Gunners ne daga Sao Paolo a shekara ta 2006, amma sai akan daina bashi damar buga kwallo saboda Jack Wilshere.

A kakar wasan data wuce dai wasanni 16 kacal Denilson ya bugawa Arsenal, kuma za bada aronshi zuwa wata kungiyar a can Brazil din.

Wenger yace"Denilson zai bar koma Brazil a matsayin aro".

Denilson ya bayyana cewar"Zan bar Arsenal cikin takaici saboda ina da abokai masu yawa a kulob din".

Denilson ya bugawa kulob din wasanni 153 inda ya zira kwallaye 10 amma bai taba lashe wata gasa ba.