Japan ta lashe gasar kwallon mata

japan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Japan na murnar doke Amurka

'Yan kwallon mata na Japan zasu koma gida a matsayin gwarzaye bayan lashe gasar kwallon mata ta duniya a ranar Lahadi.

A yayinda kasar ke farfadowa daga girgizar kasa da kuma guguwar tsunami, a yanzu kasar na cike da murna ne bayan doke Amurka a bugun fenariti a wasan karshen da suka buga a birnin Frankfurt na Jamus.

Kyaftin din Japan Homare Sawa wacce aka baiwa kyautar takalmin kwallo na zinare ta ce"Mun yi murnar wannan kofin, yanzu mune na farko a duniya".

A baya dai bajintar da Japan tayi shine a shekarar 1995 lokacin data tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe, kuma Japan din bata taba doke Amurka ba a fafatawar da suka yi sau 25 a baya.

Akan hanyarta na lashe gasar kwallon mata din dai, Japan ta samu galaba akan Jamus mai masaukin baki a zagayen gabda na kusada karshe sannan ta doke Sweden a zagayen kusada karshe kafin ta casa Amurka a wasan karshe a fenariti daci uku da daya.