Zamu yi 'fada har karshe' akan Fabregas-Guardiola

fabregas da Messi
Image caption Cesc Fabregas da Lionel Messi

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce kulob din zai yi 'fada har karshe' don sayen dan wasan Arsenal Cesc Fabregas.

Zakarun kwallon Turai din dai sun bada tayin fan miliyon 27 akan Fabregas a watan Yunin bana amma dai Gunners taki amincewa.

Guardiola yace"Barcelona ta bada tayi amma Arsenal bata yarda ba, daga nan zuwa 31 ga watan Agusta zamu yi kokarin cimma yarjejeniya".

Ya kara da cewar"Zamu yi fada har karshe don samun Cesc, saboda munsan zai karawa tawagarmu karfi".

Fabregas dan kwallon karamar kungiyar Barcelona ne kafin ya koma Arsenal a matsayin dan shekaru 16 a shekara ta 2003 kuma bai yi tafiya da Arsenal ba zuwa rangadin kasashen nahiyar Asiya a halin yanzu.

Darektan wasanni a Barcelona Andoni Zubizarreta ya ce abinda kulob din zai fi maida hankali shine siyen dan kwallon Chilea wanda ke taka leda a Udinese Alexis Sanchez .

Tsohon golan Spain din ya kara da cewar"Mun fahimci cewar yarjejeniyar na mataki na karshe, nan bada jimawa ba zamu sayi Sanchez".