Liverpool zata bada mamaki -Ferguson

ferguson da dalglish Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sir Alex Ferguson da Kenny Dalglish

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce yanasaran Liverpool zata kalubalanci kungiyoyi don neman lashe gasa a kakar wasa mai zuwa.

Liverpool dai ta shafe shekaru 21 bata lashe gasar premier ta Ingila ba, kuma a kakar wasan data wuce kulob din ya kasance na shida ne.

Amma Ferguson na tunanin cewar Liverpool a karkashin Kenny Dalglish zata yi babban barazana a kakar wasa mai zuwa.

Ferguson yace"Liverpool tayi batar dabo, amma a yanzu ta gano hanya".

A cewar kocin Red Devils din kokawar lashe gasar premier ta Ingila a badi na tsakanin kulob biyar wato United da Chelsea da Arsenal da kuma Manchester City.

Ferguson ya kara da cewar ya tunanin cewar Andre Villas-Boas zai fuskanci kalubale mai girma a Chelsea.

Chelsea zata fuskanci United a gasar premier a karon farko a filin Old Trafford a ranar 18 ga watan Satumba sai kuma United din ta tafi Anfield don karawa da Liverpool a ranar 15 ga watan Oktoba.