Sunderland ta kulla yarjejeniya da Kotoko

Asante Kotoko Hakkin mallakar hoto b
Image caption Asante Kotoko

Sunderland ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kungiyar Asante Kotoko ta Ghana don bunkasa kwallon kafa a nahiyar Afrika.

Sunderland din zata taimakawa Kotoko wajen yadda za a dinga horadda 'yan kwallo da kuma nunawa matasa dabarar kwallon kafa.

Zata kuma taimakawa kulob din na Kumasi wajen yadda harkar kwallonta zai bunkasa.

Anata bangaren Kotoko zata taimaka wajen tallata Sunderland a nahiyar Afrika.

Shugaban Sunderland Niall Quinn wanda ya karbi bakuncin tawagar 'yan Ghana din ya ce "hadin gwiwar zai taimakawa kulob din biyu".

Sunderland nada dan kwallon Ghana Asamoah Gyan da kuma John Mensah da Sulley Muntari suna taka mata leda.