Ghana zata tura likitoci don duba Essien

essien
Image caption Micheal Essien

Hukumar kwallon dake kula da kwallon kafa a Ghana GFA zata tura likitocinta zuwa Ingila don su duba tsananin raunin Micheal Essien don yanke hukunci akan dan wasan saboda gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a badi.

Dan kwallon Chelsea din zai shafe watanni shida yana jinya sakamakon raunin daya ji a wajen horo a Stamford Bridge.

Wannan ne karo na uku da dan wasan zai yi jinya mai tsawo a cikin shekaru uku, saboda bai buga gasar cin kofin duniya ba a shekara ta 2010 saboda rauni.

Kakakin GFA din Randey Abbey ya ce basu yanke kauna akan Essien ba, har sai likitocinsu sun bada rahoto akai.

Essien ya koma Black Stars ne a watan Yuni, bayan hutu na watannni 17 saboda kokarin ya warke sarai kafin ya bugawa kasar kwallo.