Uruguay ta doke Peru a gasar Copa America

suarez da forlan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luis Suarez da Diego Forlan

Luis Suarez ya tsallakar da Uruguay zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen kudancin Amurka wato Copa America, bayan yaci kwallaye biyu a wasansu da Peru inda aka tashi biyu da nema.

Suarez ya zira kwallayen a cikin mintuna biyar bayan an dawo hutun rabin lokaci, kuma a yanzu ya kamo Sergio Aguero a yawan kwallaye a gasar wato uku.

Peru dai ta samu matsala a wasanne bayan da aka kori kyaftin dinta Juan Manuel Vargas.

Uruguay zata buga wasan karshe na da duk kasar data samu galaba a wasa tsakanin Paraguay da Venezuela a yayinda ita kuma Peru zata hadu da duk kasar data gamu da rashin nasara a wasan rige rigen zama na uku.