Banason 'cacar baki' da Wenger akan Fabregas-Xavi

xavi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Xavi Hernandez

Dan kwallon Barcelona Xavi ya ce bayason "cacar baki" da kocin Arsenal Arsene Wenger akan makomar Cesc Fabregas.

A makon daya gabata ne Wenger yace Xavi ya nuna "raini" akan shawarar cewar Fabregas na shan wuya akan komawarsa a Nou Camp.

Amma Xavi ya kare kalamansa akan cewar"yana kokarin kare hakkin Cesc da Barca ne".

Fabregas dan kwallon karamar kungiyar Barcelona ne kafin ya koma Arsenal a shekara ta 2003.

A ranar Talata ne kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce kulob din zai yi fada har karshe don sayen Fabregas bayan, Arsenal taki amincewa da tayin fan miliyon 27 akan dan wasan.

Wenger na kokarin shawo kan kyaftin dinsa ya cigaba da kasancewa a Emirates don ya lashe gasar premier da suka shafe shekaru bakwai da suka wuce.

A halin yanzu dai Arsenal ta sayarda Gael Clichy ga Manchester City amma ta siyo Gervinho daga Lille da kuma Carl Jenkinson daga Charlton Athletic .