Capdevila ya koma Benfica daga Villareal

 Joan Capdevila Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Joan Capdevila

Dan kwallo baya na Spain Joan Capdevila ya bar Villarreal ya koma Benfica a kwangilar shekaru biyu.

Benfica ta sayi dan wasan mai shekaru 33 ne wanda yarjejeniyar kwangilarsa ta hada da Euro miliyon 20.

Capdevila shine ke rike bayan Spain ta bangaren hagu kuma tare da shi kasar ta lashe gasar Euro ta 2008 dana kofin duniya a shekara ta 2010.

Dan kwallon ya bugawa Spain wasanni 57, kuma ya shafe shekaru hudu a Villarreal.

Kafin Capdevilla ya je Villareal, ya shafe shekaru bakwai tare da Deportivo La Coruna.

A kakar wasa ta bana,Benfica ta sayi Eduardo da Emerson bayan ta sayarwa da Real Madrid dan kwallonta Fabio Coentrao akan dala miliyon 43.