Bin Hammam zai gurfana a gaban kwamitin da'a

Muhammad Bin Hammam
Image caption Bin Hammam ya tsaya takarar shugabancin Fifa kafin daga baya ya janye

A ranar Juma'a ne ake sa ran tsohon dan takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta FIFA Mohamed bin Hammam zai gurfana gaban kwamitin da'a domin amsa tambayoyi game da zargin cin hanci da ake yi masa.

Ana zargin cewa Mr Bin Hammam dan Qatar kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Asiya na da hannu a baiwa jami'an hukumar yankin cin hanci a lokacin yakin neman zabe a Trinidad.

Mr Bin Hammam dai ya musanta cewa sam bai yi wani abun da bashi kenan ba.

Ya dai ce 'yan adawa ne suka yi masa fenti domin dakile shi.

An tuhumi tsohon mataimakin hukumar Fifa din Jack Warner bisa shi ma zargin cin hanci amma an yi watsi da tuhumar bayan da ya yi murabus daga harkokin kwallon kafa.

A ranar Asabar ne dai ake sa ran yanke hukunci kan binciken, wanda masu sarhi ke ganin zai yi wuya Bin Hammam ya kai labari.

Wani daftari na rahoton binciken da BBC ta samu ya nuna cewa akwai cikakkun shaidun da ke nuna cewa Bin Hammam ya yi kokarin ba da cin hanci domin a zabe shi.