Mun shirya fafatawa da kowane kulob-Casillas

casillas
Image caption Golan Real Iker Casillas

Golan Real Madrid Iker Casillas ya bayyana cewar kulob din ya shirya fafatawa akan kowanne kofi tunda yanada matasan 'yan kwallo.

Sabbin 'yan wasa kamarsu Nuri Sahin, Raphael Varane da Jose Callejon zasu goge a nan gaba, kuma a cewar Casillas duk da cewar matasa amma za a dama dasu.

Casillas yace"muna da matasan 'yan kwallo wadanda cikin 'yan shekaru masu zuwa zasu bada mamaki".

Ya kara da cewar "muna gina tawaga ce wacce a nan gaba zata mamaye ko ina a duniya".

A ranar 19 ga watan Agusta ne Real Madrid zata buga wasanta na farko a gasar La Liga ta bana tsakaninta da Athletic Bilbao.