Chelsea za ta siyo 'yan kwallo biyu-Gourlay

chelsea
Image caption Chelsea ne zakarun Ingila a 2010

Shugaban Chelsea Ron Gourlay ya ce kulob din zai sayi sabbin 'yan kwallo biyu cikin kwanaki takwas zuwa goma masu zuwa.

A halin yanzu dai anata alakanta Chelsea da 'yan wasan biyu Luka Modric da Javier Pastore.

Amma dai Chelsea da Barcelona sun amince da cinikin matashin dan kwallon Oriol Romeu akan kusan fan miliyon biyar.

Sannan kuma ana ganin cewar farashin Modric da Pastore zasu kai fiye da fan miliyon 40.

Gourlay yace"idan sabon koci yazo, zai nemi sake salon tawagarsa kuma nan da kwanaki goma Andre zai yanke hukunci".

Mataimakin shugaban Palermo Guglielmo Micciche ya ce akwai yiwuwar dan kwallonsa Javier Pastore ya hade da Chelsea.