Drogba zai sabunta kwangilarsa zuwa 2013

 Didier Drogba
Image caption Didier Drogba

Dan kwallon Chelsea Didier Drogba ya ce yanasaran sabunta kwangilarsa na karin shekara guda don cigaba da kasancewa a Stamford Bridge har zuwa shekara ta 2013.

Kyaftin din Ivory Coast wanda ya koma Blues daga Marseille a shekara ta 2004, ya bayyana cewar sun fara tattaunawa akan sabuwar kwangilar.

Drogba yace"Mun soma tattaunawa kuma tabbas zan cigaba taka leda a nan a kakar wasa mai zuwa".

A halin yanzu dai akwai hammaya matuka a bangaren gaban Chelsea saboda bayaga Drogba akwai Fernando Torres da Nicolas Anelka da kuma Daniel Sturridge.

Amma a cewar Drogba babu matsala akan wannan hammayar saboda tun shekarun baya haka lamarin yake.

Yace"haka yake lokacin Eidur Gudjohnsen yana nan da kuma lokacin Andriy Shevchenko amma kowa na samun bugawa".