Ramuwar gayya ce Fifa tayi man- Bin Hammam

blatter da hammam
Image caption A baya Blatter da Bin Hammam aminai ne

Tsohon dan takarar shugabancin Fifa Mohammed Bin Hammam ya ce dakatar dashi na mudin rai da aka yi daga harkar kwallon kafa wata dabara ce ta yin ramuwar gayya.

Dan kasar Qatar din mai shekaru 62 a ranar Asabar ne kwamitin da'a na Fifa ya kamashi da laifin yin kokarin bada cin hanci.

Amma dai Bin Hammam wanda ya kalubalanci shugaban Fifa Sepp Blatter ya shaidawa BBC cewar "dakatarwar muddin rai nake saran za ayi mani, saboda ramuwar gayya ce".

Ya kara da cewar "an yanke hukunci ba tare da fara binciken ba".

Kwamitin da'a na Fifa a zaman da yayi na kwanaki biyu ya zargi Bin Hammam da kokarin sayen kuri'a a zaben Fifa na watan Yuni, amma daga bisani sai Hammam din ya janye.

Hakan ne ya baiwa Sepp Blatter damar yin takara babu hammaya, kuma Hammam ya kasance babban jami'in Fifa na farko cikin shekaru 107 da kafuwarta da aka dakatar dashi.

Tsohon shugaban kwallon nahiyar Asiya bai halarci taron kwamitin da'a ba a Zurich amma ya ce zai daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin wasanni-Cas inda yake ganin za a yi mashi adalci.