Bin Hammam zai daukaka kara

Bin Hammam Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bin Hammam ya taka rawa wajen kai gasar cin kofin duniya ta 2022 Qatar

Tsohon Shugaban Hukumar kwallon kafa a nahiyar Asiya Muhamman bin Hamman ya ce zai daukaka kara kan hukuncin dakatar da shi da aka yi daga duk wani abu dake da nasaba da wasa har iya rayuwarsa.

A ranar Asabar ne dai kwamitin da'a na FIFA ya yanke hukunci kan zargin da ake wa Bin Hamman na bada cin hanci a kokarin sayan kuri'u a lokacin zaben shugabancin hukumar FIFA, domin doke shugaban hukumar Sepp Blatter.

Shugaban Kwamitin da'a na hukumar ya ce an dakatar da Bin Hammam daga taka rawa a duk wani nau'in abu da ya shafi kwallon kafa a gida da waje.

Wala Allah ta bangaren zartarwa ko wasannin ko ma meye, har iya rayuwarsa.

Masu sharhi dai na yiwa wannan hukunci kallo ta fuskoki da dama.

Bin Hammam ne kadai ya fito ya bayyana aniyar kalubalantar Seff Blatter kafin daga bisani ya janye a zaben shugabancin Fifa da aka gudanar a watan Yunin da ya gabata.