Beckham ya kare baran-baramar Balotelli

Beckham da Balotelli Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Beckham da Balotelli

David Beckham ya kare Mario Balotelli akan baran-baramar da yayi a wasan tsakanin Manchester City da LA Galaxy.

Amma dai kocin City Roberto Mancini ya nuna bacin rai akan kwarewar dan wasan mai shekaru 20 wanda a gaban raga ya juya baya don ya saka kwallo da dunduniyar kafarsa.

Beckham yace "dana sake duba wannan lamarin, sai na fahimci cewar ya dauka cewar yayi satan gola ne".

Ya kara da cewar"Mario babban dan wasa ne duk da cewar matashi ne".

Tsohon kyaftin din Ingilan wanda ya taka leda a Manchester United ya ce Balotelli ya kara gogewa.

A lokacin wasan dai, nan take Mancini ya fidda Balotelli daga wasan saboda a tunaninsa dan wasan baya maida hankali.