Batista ya sauka daga mukaminsa na kocin Argentina

Image caption Tsohon kocin Argentina, Sergio Batista

Sergio Batista ya yarda ya ajiye aikinsa a matsayin kocin Argentina, bayan an fidda Argentina a wasan dab da kusa dana karshe a gasar Copa America.

Kasar Uruguay ce ta fidda Argentina wadda itace mai masaukin baki a bugun fenarity a wasan dab da kusa dana karshe.

Batista, mai shekarun haihuwa 48, ya jagoranci kungiyar ne na tsawon shekara guda, da farko a matsayin kocin wucin gadi a lokacin da aka sallami Diego Maradona bayan gasar cin kofin duniya.

Hukumar kwallon Argentina ta ce bata kori Batista ba, amma ta janye kwantaragin da ta baiwa kocin.