Ba zan siyo karin 'yan kwallo ba-Ferguson

fergie Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce da kamar wuya ya kara siyo sabbin 'yan kwallo kafin wasansu na Community Shield tsakaninsu da Manchester City a Wembley.

Kawo yanzu dai ya siyo Ashley Young da Phil Jones da kuma gola David de Gea.

Sannan kuma ana alakanta dan kwallon Inter Milan Wesley Sneijder da komawa United.

Amma Ferguson ya ce " A halin yanzu bana tunanin wani kari saboda irin dan kwallon da muke nema babu shi".

Da yake jawabi kafin wasansu a Amurka, Ferguson ya ce "mun rasa 'yan kwallo biyar saboda sun wuce shekaru 30".

Ritayar Paul Scholes ta janyo ana tunanin cewar Wesley Sneijder ko Samir Nasri ko kuma Luka Modric ne zasu iya maye gurbinsa.

Amma dai Ferguson ya nisanta kanshi da Sneijder inda yace"baida sha'awa akanmu".