West Brom na zawarcin Foster daga Birmingham

foster
Image caption Ben Foster

BBC ta fahimci cewar West Bromwich Albion zata sayi golan Birmingham Ben Foster.

Rahotanni sun nuna cewar ana tattaunawa tsakanin kulob din biyu akan dan wasan.

Kocin Westbrom Roy Hodgson na bukatar sabon gola bayan Scott Carson ya koma kungiyar Bursaspor ta Turkiya.

Baya ga Foster, ana alakanta West Brom din da golan West Ham Robert Green.

Foster mai shekaru 28 ya bayyana cewar yanason cigaba da taka leda a Birmingham.