Zamu kara siyo dan kwallo daya a United-Gill

gill
Image caption David Gill

Shugaban Manchester United David Gill ya ce kulob din zai siyo karin dan kwallo guda daya kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo.

Ko da yake dai kocin United Sir Alex Ferguson a ranar Litinin ya bayyana cewar da kamar wuya su kara wani dan kwallo a kwanan nan.

A cewar Gill a yanzu ba suna cinikin wani dan kwallo bane, amma dai watakila su kara cefano dan wasa.

Zakarun kwallon gasar premier din wadanda suka yi rangadi a Amurka na makwanni uku, a halin yanzu sun siyo Ashley Young daga Aston Villa, da dan Blackburn Rovers Phil Jones sai kuma gola David de Gea daga Atletico Madrid.