Chelsea ta kai kara akan 'zagin' Benayoun

benayoun
Image caption Dan Isra'ila Yossi Benyoun

Chelsea ta kai kara wajen hukumar kwallon Malaysia akan nuna kin jinin dan kwallonta Yossi Benayoun.

Dan kwallon Isra'ila mai shekaru 31 an yi masa ihu da zarar ya taba kwallo a wasansu da Malaysia a ranar 21 ga watan Yuli. Chelsea ta ce "Mun yarda an nunawa Yossi bambamci daga wajen magoya baya a lokacin wasan".

A cewar kulob din ba zai yarda da wannan abu ba, don a sabawa dokar kwallon kafa.

Chelsea ta ce bata kai kara a lokacin da abin ya faru ba saboda bata san dalilan zagin ba amma data sake duba bidiyon wasan sai ta gano cewar nuna kin jini ne.