An dakatar da El-Hadji Diouf na tsawon shekaru biyar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption El-Hadji Diouf

Hukumar kwallon kafa a Senegal ta dakatar da dan wasan Blackburn Rovers' El-Hadji Diouf daga duk wata harkar kwallon kafa na tsawon shekaru biyar.

Hukumar dai ta dakatar da dan kwallon ne saboda zargin cin hanci da ya yi wa wasu jami'an Hukumar.

Sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce: "Mun dakatar da Diouf daga duk wani harkar kwallon kafa na tsawon shekaru biyar."

Diouf ya fusata ne dai bayan yaki ya bayyana a gaban kwamitin ladabatarwar hukumar a makon daya gabata.

Kwamitin dai na son ji daga dan wasan ne game da zargin da ya yi a wani gidan radiyon Faransa, wanda ya ce harkar kwallon kafa a Africa na fama da rashawa dumu-dumu.