An sabunta: 28 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 15:59 GMT

Emmanuel Emmenike ya koma Spartak Moscow

emenike

Emmanuel Emenike

Dan kwallon Najeriya Emmanuel Emenike ya bar kungiyar Fenerbahce ta Turkiya ya koma Spartak Moscow ta Rasha.

Emenike mai shekaru 24 'yan sanda Turkiya sun yi mashi tambayoyi a watan daya gabata akan batun joge a wasa.

A halin yanzu dai Fenerbahce na fuskantar barazanar kwace mata kofin gasar 2011 a yayinda ake cigaba da bincike akan saida wasa a lokacin gasar kwallon kasar a kakar wasan data wuce.

Ita kuma Spartak Moscow itace ta biyar akan tebur na gasar Rasha.

Emenike yayi sunane a Turkiya a kulob din Karabükspor kuma yana cikin tawagar Najeriya da zata kara da Ghana a wasan sada zumunci a wata mai zuwa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.