Majalisar Dokokin Burtaniya ta nemi gyara a harkar kwallon kafa

Majalisar Dokokin Burtaniya ta yi kira ga Hukumar kwallon kafa ta kasar da ta yi gyara a harkar kwallon kafa domin ciyarda wasan gaba a kasar.

Wani rahoto da Majalisar ta fitar ya nemi da a sa ido sosai a harkar kwallon kafa musamman ta fanin kudi, saboda kungiyoyi su daina shiga matsalar bashi.

Wani dan Majalisa John Whittingdale ya ce; " Dolene ayi sauyi a harkar kwallon kafa, saboda kwallon kafa a Ingila ya yi armashi."

Portsmouth ce kungiyar farko a gasar Premier ta kasar da ta fara shiga matsalar bashi a watan Fabrairun shekarar 2010.