Gerrard zai cigaba da jinya har Satumba

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard

Ana saran kyaptin Liverpool Steven Gerrard ya koma taka leda a watan Satumba saboda rauni.

Gerrard mai shekaru 31 zai shafe kwanaki a asibiti yana magani kafin ya koma gida ya cigaba da jinya.

Tun a watan Maris Gerrard ya ke fama da rauni.

Gerrard bai je rangadin Liverpool a nahiyar Asiya ba kuma ba zai buga wasan bude gasar premier tsakaninsu da Sunderland ba a filin Anfield.

Rauni ya tasa Gerrard a gaba, saboda a kakar wasan data wuce wasanni 21 cikin 38 kawai ya buga na gasar premier.