Shakku kan makomar kocin Botswana

Kocin Botswana Stanley Tshosane
Image caption Tshosane ya jagoranci Botswana zuwa gasar cin kofin Afrika

Har yanzu ba a baiwa kocin Botswana Stanley Tshosane sabuwar kwantiragi ba duk da ya jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a karon farko.

Kocin wanda shi ne ya fi kowanne taka rawa a tarihin kasar, na shiryawa gasar ta watan Janairu - amma banda gasar cin kofin duniya ta 2014.

"Ba zan yi magana a kanta sosaiba, saboda bani da tabbas ko nine koci a lokacin, saboda kwantiragi na za ta kare a watan Maris," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Zan so na ci gaba amma hakan zai dogara ne kan Hukumar kula da kwallon kafa ta Botswana."

Amma duk da haka Tshosane ne ya sa ido kan rukunin gasar share fagen gasar cin kofin duniyar da aka raba, inda kasar za ta kara da Afrika da Kudu da Afrika ta Tsakiya da Somalia ko Ethiopia.

"Rukuninmu na gasar share fagen yana da zafi, amma bai kai zafin na gasar share fagen gasar kasashen Afrika na 2012 ba."