An sabunta: 1 ga Agusta, 2011 - An wallafa a 13:49 GMT

Brazil 2014: Malawi ta gargadi Najeriya

Tawagar kwallon Malawi

Tawagar kwallon Malawi na taka rawa a baya-bayan nan

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Malawi ya gargadi Najeriya da kada ta raina kasarsa a karawar da za su yi a gasar share fagen shiga gasar cin kofin duniya.

Ana saran Super Eagles ne za su lashe rukunin na F wanda ya hada da kasashen Seychelles da Kenya da Djibouti ko Namibia.

Amma Walter Nyamilandu na ganin Malawi ba kanwar lasa bace don haka za ta iya baiwa Najeriya mamaki.

"Najeriya ce kan gaba a rukunin, amma muma ba kanwar lasa bane," a cewar Nyamilandu.

Nyamilandu ya kara da cewa kungiyar kwallon kafa ta Malawi wacce aka fi sani da Flames sun nuna kansu bayan da suka samu damar shiga gasar cin kofin kasashen Afrika bara a Angola.

Duk da cewa ya bayyana kwarin da Super Eagles ke da shi, Nyamilandu ya shaida wa BBC cewa tawagar ta Samson Siasia na da rauni ta wani bangaren.

"Rukuni ne mai hadarin gaske; muna ganin muna da damar kai labari idan muka shirya sosai."

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.