Sneijder bai fitar da ran komawa United ba

Wesley Sneijder
Image caption Wesley Sneijder yana haskakawa sosai a Inter Milan

Dan wasan Inter Milan Wesley Sneijder ya ki bayyana cewa ba zai koma Manchester United ba, a yayin da rade-radi ke karuwa kan yiwuwar komawarsa Old Trafford.

"A kwai yiwuwar komai na iya faruwa, amma za mu jira mu gani," a cewarsa.

Dan wasan mai shekaru 27, ana yi masa farashi kan fan miliyan 35 amma yana da albashin da ya kai fan 250,000 a mako.

Kocin United Sir Alex Ferguson ya musanta rahotannin da ke cewa an yi yarjejeniya kafin a cimma matsaya kan farashi.

Kawo yanzu Manchester United ta sayi mai tsaron gida David de Gea da dan wasan baya Phil Jones da kuma na gaba Ashley Young, amma tana bukatar dan tsakiya bayan da Paul Scholes ya yi ritaya.

Idan har cikin zai yi wu, to mai yiwuwa dan wasan ya hakura ya rage albashin da ya ke karba domin komawa United din.