Zoltan Gera ya koma West Brom

Image caption Zoltan Gera

Zoltan Gera ya koma kungiyar West Bromwich Albion na tsawon shekaru biyu.

Dan wasan wanda dan asalin Hungry ne, ya takawa kungiyar West Brom leda ne tsawon shekaru uku, kafin ya koma Fulham a watan Yunin shekarar 2008.

Kwantaragin dan wasan ya kare ne da Fulham a karshen kakar wasan bara.

A lokacin da dan wasan ke taka leda a Fulham, Gera, mai shekarun haihuwa 32, ya taka leda karkashin kocuin West Brom na yanzu, wato Roy Hodgson.

Hodgson ne kuma ya sayo dan wasan daga West Brom zuwa Fulham.