'Wesley Sneijder zai taka leda a China' - Kocin Inter Milan

Image caption Wesley Sneijder

Inter Milan ta ce Wesley Sneijder zai taka leda a ranar asabar a gasar Italian Super Cup duk da rahotannin dake nuni da cewa dan wasan zai koma kungiyar Manchester United.

Rahotannin dai sun ce dan wasan mai shekarun haihuwa 27 sai koma Manchester United a kudin fam miliyan 35.

Amma dan wasan dai zai yi tafiya China inda kungiyarsa za ta fafata da AC Milan.

"Zai taka mana leda, yana horo da mu kuma zai buga mana wasa a ranar asabar," In ji Kocin Inter Gian Piero Gasperini.

Ya kara da cewa: "Bamu da matsala da Sneijder."