Rebecca Adlington za ta kara kaimi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rebecca Adlington

Rebecca Adlington wadda ta lashe kyautuka biyu a gasar World Championships ta ce har yanzu akwai sauranta, domin kuwa za ta kara kaimi a wasanni Olympics da za'a yi a birnin Landan a badi.

Rebecca wadda take wasan ninkaya, 'yar Burtaniya ce kuma ta yi nasara a gasar World Championships da ta halarta a Shanghai a makon daya gabata.

"Saboda gasar da na halarta, ina kara samu kwarin gwiwa a duniya." In ji Adlington.

"Har wa yau ina kokarin in kara inganta yadda nake ninkaya, musamma ma wajen kara sauri."

Adlington ta lashe zinari a ninkayan zangon minta dari takwas da kuma azurfa a na zangon mita dari hudu a gasar da ta halarta a China, amma ta gaggara kaiwa wasan kusa dana karshe a zangon mita 200.