Kotu ta sauke Shugaban gasar Premier ta Najeriya

Hakkin mallakar hoto ibrahim
Image caption Davidson Owumi

Wata babbar Kotun tarraya a Abuja ta sauke Shugaban Hukumar gasar Premier ta Najeriya Davidson Owumi daga mukaminsa.

Har wa yau, Kotun ta umarci, Hukumar da ta gudanar da sabuwar zabe domin cike gurbin kujerar shugaban Hukumar, nan da kwanaki 30.

An zabi Owumi ne a watan Mayun shekarar 2010, amma abokin takararsa Victor Baribote, ya kalubalanci zaben da cewa Owumi bai cancanta ya tsaya takara ba.

Batun dai ya kai gaban Hukumar kwallon kafan Najeriya, wadda ta nada wani kwamitin domin ya duba lamarin.

Kwamitin bayan ya gama bincikensa ya umarci da a sake gudanarda da wani zaben, amma sai Owumi ya ki ya amince inda ya ce Hukumar kwallon Najeriya ba ta da hurumin cewa a sake wani zaben.

Alkalin kotun dai Justice Kolawole ya yanke hukuncin cewa Hukumar NFF na da hurumin cewa a sake wani zaben, saboda ita ke da duk wani iko da ya shafi harkar kwallon kafa a kasar.