Colombia 2011: An doke Mali da Kamaru

Colombia 2011: An doke Mali da Kamaru Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Mali Sekou Diallo ya ce 'yan wasansa ba su da kwarin gwiwa

Mali ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Colombia a rukunin A, yayin da Kamaru ta sha kashi karo na biyu a hannun Portugal da ci 1-0 a rukunin B. Colombia ta zira kwallayenta ne ta hannun Jose Valencia kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan James Rodriguez ya zira ta biyu a mintin karshe na wasan, abinda ya basu damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Kocin Mali Sekou Diallo ya ce 'yan wasansa ba su da kwarin gwiwa.

"Jikinmu ya mutu tun bayan da muka sha kashi a wasan farko, inda Koriya ta Kudu ta doke mu da ci 2-0," a cewarsa.

"Mun sha kashi ne a hannun babbar kungiya Colombia, wacce ta samu goyon baya daga magoya bayanta a matsayinta na mai masaukin baki."

A daya wasan da aka yi a rukunin na A, Faransa ta doke Koriya ta Kudu da ci 3-1.

Nelson Oliveira ne ya zira kwallo a minti na 19 wacce ta baiwa Portugal damar lashe Kamaru da ci daya mai ban haushi.

Kamaru ta kammala mintina 19 na karshen wasan ne da 'yan wasa goma bayan da aka baiwa dan bayanta Ghislain Mvom jan kati.