Colombia 2011: Najeriya ta lallasa Croatia

Colombia 2011: Najeriya ta lallasa Croatia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Uche Nwofor ya shigo daga baya amma ya zira kwallaye biyu

Najeriya ta zira kwallaye 5 a wasanni biyu a jere a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 20 bayan da ta lallasa Colombia da ci 5-2 a safiyar Alhamis.

Wannan sakamakon ya nuna cewa kungiyar ta Flying Eagles ta zamo ta farko daga cikin wakilan Afrika da suka samu kaiwa ga zagaye na biyu a gasar.

Olarenwaju Kayode da Terna Suswan su ne suka fara zira kwallaye tun a zagayen farko na wasan kafin Ahmed Musa ya zira daya, sannan kuma Uche Nwofor ya zira guda biyu.

Ivan Lendric da Andrej Kramaric su ne suka zirawa Croatia na ta kwallayen.

Kocin Najeriya John Obuh ya ce sakamakon wasan bai bayyana ainahin abin da ya faru a filin wasanba.

"Mun yi hasashen za su taka rawar gani kuma sun yi hakan," a cewarsa.

"Wasan ya yi mana tsauri da yawa, amma mun yi sa'a mun kai ga gaci.

A daya wasan da aka fafata a rukunin na D, Saudi Arabia ta lallasa Guatemala da ci 6-0.

Wasan Najeriya na karshe a rukunin shi ne tsakaninta da Saudi Arabia ranar Asabar, kuma shi ne zai fayyace wanda zai jagoranci rukunin - duka kungiyoyin sun samu nasara a wasanni biyun da suka buga.

Sai dai Najeriya na kan gaba saboda ta fi zira kwallaye da yawa.