City ta karawa Tavez lokacin hutu

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dade ana sa'insa kan makomar Carlos Tevez

Manchester City ta ce ta karawa Carlos Tevez lokacin hutunsa, abin da ya sa a yanzu ake saran zai dawo domin horo tare da sauran 'yan wasa ranar Litinin.

Wannan na nufin Tavez ba zai taka leda a wasan da City za ta fafata da Manchester United na cin kofin Community Shield ba da za a yi a filin wasa na Wembley ranar Lahadi.

A baya City ta ce zai dawo ne ranar Alhamis, sai dai BBC ta fahimci cewa har zuwa ranar Laraba Tavez baya Burtaniya.

A watan Juni dan wasan mai shekaru 27 ya ce ba zai kara komawa garin Manchester ba "koda kuwa domin hutu".

Daga bisani kuma ya nemi a kyale shi ya bar kulob din sai dai yunkurin sayensa da Corinthians na Brazil suka yi kan fan miliyan 40 ya ci tura.

"An karawa Carlos kwanaki domin ya dawo har zuwa ranar Litinin, wato kwanaki 21 bayan fitar da Argentina daga gasar Copa America," a cewar mai magana da yawun kulob din.

Baya ga Corinthians, ana kuma danganta dan wasan na Argentina da yiwuwar komawa Inter Milan da Real Madrid.