Ingila ta gayyaci Phil Jones

Phil Jones Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jones ya koma United ne daga Blackburn a watan Yuni

An gayyaci dan wasan baya na Manchester United Phil Jones cikin jerin 'yan wasa 30 domin shiryawa wasan sada zumuntar da Ingila za ta kara da Holland ranar Laraba.

Jones, mai shekaru 19, ya koma United ne daga Blackburn a kan fan miliyan 17 a watan Yuni.

Har yanzu dai ba a gayyaci tsohon kyaftin David Beckham ba, duk da haskakawar da yake yi a kulob dinsa na LA Galaxy. A karshen mako ne ake saran kociya Fabio Capello zai rage adadin 'yan wasan zuwa 23.

Har yanzu ba a bayyana sunayen a filiba. Hukumar kwallon kafa ta FA ce ke tuntubar 'yan wasan da kuma kulob dinsu domin sanin ko za su samu damar taka wasan. Capello ya ce yanzu ba lokaci ba ne na sauye-sauye ganin cewa ba a fara gasar cin kofin Premier ba.