Zakarun Turai: Udinese za ta kara da Arsenal

Zakarun Turai: Udinese za ta kara da Arsenal
Image caption Za a buga wasannin ne a ranakun 16/17 da kuma 23/24 na watan Agusta

Arsenal za ta fafata da Udinese na Italiya a wasan share fage na shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Arsenal ce za ta karbi bakuncin wasan farko a ranar Talata 16 ga watan Agusta, inda za a yi wasa na biyu kwanaki bakwai baya.

Bayern Munich na Jamus za su kara da FC Zurich na Switzerland, FC Twente na Holand za ta fafata da Benfica na Portugal.

Yayin da Lyon na Faransa za su kece raini da Rubin Kazan na kasar Rasha.

Cikakken teburin wasannin da za a buga:

Wisla Krakow da Apoel Nicosia

Maccabi Haifa da Genk

Dinamo Zagreb da Malmo FF

FC Copenhagen da Plzen

BATE da SK Sturm Graz

Odense BK da Villarreal

FC Twente da Benfica

Arsenal da Udinese

Bayern Munich da FC Zurich

Lyon da Rubin Kazan

Za a buga wasannin ne a ranakun 16/17 da kuma 23/24 na watan Agusta.