U 20:Najeriya ta lallasa Saudi Arabia

flying eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya ta casa Saudi Arabia daci biyu da nema

Najeriya ta samu nasara a wasanta na uku a gasar cin kofin kasashen duniya 'yan kasada shekaru 20 bayan ta doke Saudi Arabia daci biyu da nema.

Ahmed Musa da Olarenwaju Kayode ne suka ciwa Najeriya kwallaye.

A yanzu Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na biyu kuma zata hadu da Ingila a ranar Laraba mai zuwa.

Ingila ta tsallake zuwa zagaye na biyu bayan ta tashi babu ci a wasaninta uku.

Saudi Arabia ta karke ta biyu a rukunin kuma zata buga da Brazil a wasan zagaye na biyu.

Spain da Colombia sune sauran kasashen da suka tsallake zuwa zagaye na gaba.

Rukunin D: * Najeriya maki 9 * Saudi Arabia maki 6 * Guatemala maki 3 * Croatia maki 0