Manchester United ta doke City a Community Shield

nani
Image caption Nani

Nani ya zira kwallaye biyu a yayinda Manchester United ta doke Manchester City ta kuma lashe kofin Community Shield.

Joleon Lescott ne ya ciwa City kwallon farko kafin Edin Dzeko yaci na biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Chris Smalling ya farkewa United kwallo daya sannan daga bisani Nani ya ciwa United kwallonta na biyu.

Ana sauran 'yan mintuna a tashi wasan sai Nani ya yanka golan City Joe Hart ya ciwa United kwallon daya bata nasara a wasan.