Dan wasan Chelsea Zhirkov ya koma Anzhi

Yuri Zhirkov
Image caption Yuri Zhirkov

Kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha ta siyo Yuri Zhirkov daga Chelsea akan kwangilar shekaru hudu.

Rahotanni sun nuna cewar Anzhi ta biya Chelsea fan miliyon 13.2 akan Zhirkov kuma akwai yiwuwar za a dinga biyanshi Euro miliyon biyar da rabi a matsayin albashi wato dan wasan da yafi kowanne karbar albashi a Rasha kenan.

Ana saran zai buga wasansa na farko ne tsakaninsu da Spartak Moscow.

Kocin Anzhi Gadzhi Gadzhiev yace "Yuri kwararren dan kwallon kuma naji dadin siyenshi".

Shekaru biyu da suka wuce Chelsea ta biya CSKA Moscow fan miliyon 8 million akan Zhirkov.