Yan wasa da dama ba za su buga wasan Najeriya da Ghana ba

Peter Odemwingie
Image caption Peter Odemwingie na ci gaba da murmurewa daga rashin lafiya

Rashin bisa da raunuka ya hana 'yan wasan Najeriya da dama buga wasan sada zumuntar da kasar za ta fafata da Ghana ranar Talata a Ingila.

Wannan wasa dai na daya daga cikin wasanni 13 da kasashen Afrika za su fafata, domin shirya wa wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afrika a watan gobe.

Tawagar ta Najeriya ta samu koma-baya bisa matsalar bisa da kuma rashin lafiyar 'yan wasa - a wasan da za a kara a filin wasa na Watford Vicarage.

Vincent Enyeama da Victor Obinna da Ekigho Ehiosun da Ambrose Efe da kuma Fengor Ogude duka ba za su fafata ba, bayan da suka kasa samun bisar shiga Burtaniya saboda wasu dalilai.

Akwai yiwuwar John Mikel Obi ma ba zai taka leda ba, bayan da ya samu rauni a wasan da Chelsea ta buga da Rangers, yayin da Peter Odemwingie ke ci gaba da murmurewa.

A yanzu an gayyaci Peter Utaka da kuma Chibuzor Okonkwo domin maye gurabensu.

Jerin wasannin da za a fafata:

09 Agusta:

Nigeria da Ghana, Watford, London - Laraba

10 Agusta:

Senegal da Morocco, Dakar

South Africa da Burkina Faso, Johannesburg

Gabon da Guinea, Paris

Equatorial Guinea da Guinea-Bissau, Lisbon

Zimbabwe da Zambia, Harare

Tunisia da Mali, Monastir

Ivory Coast da Israel, Geneva

Botswana da Kenya, Gaborone

Liberia da Angola, Monrovia

Malta da Central African Republic, Malta

The Gambia da DR Congo, Banjul

Sudan da Tanzania, Khartoum