Laurent Blanc ya kira Clichy a madadin Evra

clichy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gael Clichy

Kocin Faransa Laurent Blanc ya kira dan kwallo Manchester City Gael Clichy don maye gurbin dan wasan Manchester United Patrice Evra a wasansu na sada zumunci tsakaninsu da Chile.

Evra ya ji ciwo a gwiwarsa a wasan Community Shield da United ta lallasa City daci uku da biyu.

A ranar Talata ne aka gwada lafiyar Evra sakamakon daya nuna cewar ba zai iya buga wasan na ranar Laraba a Montpellier.

Clichy da farko bayan cikin tawagar da Blanc ya gayyata don fuskantar Chile saboda yafi son amfani da dan wasan Barcelona Eric Abidal da kuma Evra a bangaren baya na hagun Faransa.

Clichy mai shekaru 26 ya bugawa Faransa wasa na farko a watan Satumban 2008, amma kuma baya samun damar takawa kasar leda sosai.