An dage wasan Ingila da Holland

Tawagar Ingila
Image caption Rahotanni sun ce babu abin da ya samu 'yan wasan Ingila

Tarzomar da aka shafe kwanaki uku ana yi a birnin London ta sanya an dage wasan sada zumuntar da aka shirya yi tsakanin Ingila da Holland a filin wasa na Wembley.

A ranar Talata Hukumar kula da kwallon kafa ta FA ta tabbatar da hakan a shafinta na intanet.

Wasannin Carling Cup da aka shirya yi a Charlton da West Ham da Crystal Palace da kuma Bristol City duka an dage su.

Sai dai jami'ai a Edgbaston sun shaida wa BBC cewa za a gudanar da wasan kuriket tsakanin Ingila da India da aka shirya yi a Birmingham ranar Laraba kamar yadda aka tsara.

Wakilin BBC Joe Wilson ya ce a ranar Talata an nemi otel-otel din da suke kusa da su rufe kofofinsu.

Ya bayyana a shafinsa na Twitter: "Helikwafta na shawagi a dab da otel din da 'yan wasan Ingila ke zaune. Na yi magana da jami'in tsaro na tawagar Ingila, kuma ya ce duka 'yan wasan lafiyarsu lau."